
Limamin babban masallacin Juma’a na garin Suleja dake jihar Niger, Sheikh Dahiru Shuaibu ya mutu ranar Asabar awanni kadan bayan ya dawo daga aikin Hajji a kasar Saudiya.
Abduljalil Dahiru Daya daga cikin iyalan , mamacin ya ce limamin wanda ya dawo daga Saudiyya a ranar Asabar wajen karfe 09:00 na safe ya mutu sanadiyar bugawar zuciya da misalin karfe 11:00 na dare a gidansa
Ya ce “Ina daya daga cikin iyalan da suka je filin jirgin saman Abuja da safiyar ranar Asabar domin tarbar liman. Amma da wajen karfe 11:00 na dare sai aka kira ni a cewar liman ya rasu.”
Tuni aka yi Jana’izar marigayin inda aka binne gawarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada a makabartar musulmai dake Suleja