An kasa cimma matsaya a sulhun da jam’iyyar APC maiu mulki a Najeriya ke ƙoƙarin yi tsakanin ɓangaren gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Shugaban riƙo na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe Alhaji Maimala Buni ne ya jagoranci wasu gwamnoni wajen ganawa da tsagin jam’iyyar a jihar Kano da ke ƙarƙashin tsohon gwamna, Senata Ibrahim Shekarau da da aka fi sani da G7 da nufin sulhunta tsakaninsu da tsagin Gwamna Ganduje.
Sun yi zaman ne a Abuja, amma rahotanni na nuna cewa da yiwuwar su ci gaba da ganawar.
Hon Alhassan Uba Idris dan tsagin G7, kuma Ibrahim Isa ya tuntube shi don jin yadda zaman sulhun ya kasance:
Hon Alhassan: Sun yi amfani da wasu fitattun mutane a ƙasa da ake jin maganarsu aka kira shugabanninmu na G7 sun zauna jiya sun tattauna, amma ba a cimma matsaya ba.
An ɗage tattaunawar zuwa ranar Talata, za mu zo da matsayarmu, idan an samu daidaito to shi kenan.
Ibrahim Isa: Me ya hana sasantawar?
Hon Alhassan: Abin da ya hana sasantawar babu wanda zai yarda a turo wasu ƴan takara a ce su za su zauna su yi sulhu a madadin gwamnati da gwamnatin jihar Kano.
Shi jagoran gwamnatin jihar kano shi ya kamata a yi gaba da gaba da shi da shugabannin jam’iyya da kuma gwamnonin da suka zo wannan wuri domin akwai gwamononi irinsa.
Amma ba ya turo wasu mutane da muke zaton in an tatauna ma idan sun koma zai ce ba da yawunsa suka yi magana ba.
Ibrahim Isa: Wane tayi aka yi muku da bai kwanta muku ba?
Hon Alhassan: Tayin da aka yi cewa a raba jami’iyya 50-50, mu kuma yanzu da jam’iyya ke hannunmu ba wanda za mu bai wa kashi 50, ko kashi 1 ba za mu bayar ba.
Ibrahim Isa: An tabo makomar shari’arku da ke kotu a wajen sulhun?
Hon Alhassan: Ba wanda ya taɓo makomar wannan don kowa ya san ba mu muka ɗaukaka ƙara ba.
Har muka je kotun farko da ta biyu babu wanda ya kira mu sulhu. Saboda haka hukuncin da aka yanke na hannunmu kuma shi ne abin dogaronmu cewa jam’iyya na hannumu saboda haka ba abin da ya kau da wannan.
Ibrahim Isa: Akwai yiwuwar ku haƙura da maganarku da ke kotu a wajen sulhun?
Hon Alhassan: Ba za mu yarda mu janye maganarmu daga kotu ba, sai an tabbatar jam’iyya tamu ce, shugabanci namu ne, sannan za mu je babban taron jam’iyya mun dawo, mun zauna daram dam mun buɗe sakatariya, Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya ci gaba da shugabancin jam’iyya shi ne za mu yarda da wani abu, bayan wannan babu komai.