Auren zawarawa: An gano maza da mata 18 dauke da HIV

BBC

Hukumar Hisba da ke jahar Kanon Najeriya ta tantance kimanin maza da mata dubu takwas a shirin aurar da zawarawa da gwamnatin jahar ta shirya.

Tun a ranar 12 ga watan Disambar 2018 ne dai gwamnatin jahar ta kafa wani kwamitin mai mutun 23 domin tantance wadanda ake son aurarwa.

An dai ware aurar da 3000 daga cikin 8,000, bayan gano maza da mata 18 dauke da cutar HIV da kuma ciki.

Shugaban Kwamitin aurar da zawarawan Ali baba Fagge a gama lafiya ,ya shaidawa BBC cewa gwamnati ta debo litoci daga asibiti jihar da na tarayya domin gudanar da aikin tantacewar don kaucewa fasa gurbi.

A cewarsa, matasa da dama na bukatar aure, amma rashin sukuni ya hana su, don haka ne ake tallafa musu.

Ya ce an ware masu dauke da cuta mai karya garkuwa jiki, kuma an daura su aka maganin, sannan an bukaci masu dauke da irin cutar idan su amince da juna ko kuma suna da mai son su a haka su gabatar da su sai a hada auren su.

Ali Baba ya ce akwai kalubalen da suke fuskanta saboda a wasu lokutan mata na gujewa shiga tsarin aurar da zawarawan saboda wasu dalilai da suka danganci al’ada da dai sauransu.

Karin bayani

Wannan dai ne shi ne karo na biyu da gwamnatin Abdullahi Ganduje ke tallafawa wajen yi wa mabukata aure.

A bara ma ta taimaka wa amare da angwaye fiye da 1500.

Sai dai yayin da gwamnati ke wannan agaji, a bangare guda kuma ana kuka da yadda aure ke yawan mutuwa a jihar Kanon, lamarin da wasu ke dangantawa da auren gata, inda ake wanke amare ana kai wa gidan miji ba tare da angwayen sun yi dawainiya ba, kuma irin wannan cin bulus din, a cewar masana na daga cikin dalilan da ke sa wasu mazajen suna yi wa auren rikon wulakanci, sannan kuma yana mutuwa.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...