Attahiru Jega: Tsohon shugaban INEC ya gargadi ‘yan Najeriya kan sake zaɓen APC da PDP

Jega ya ce ɓarayin PDP ne suka koma APC
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya, Farfesa Attahiru Muhammad Jega, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su dawo daga rakiyar manyan jam’iyyun ƙasar na APC da PDP, saboda yadda suka kasa taɓuka wani abun arziƙi a tsawon shekaru 20 da suka shafe suna mulki.

Yayin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Jega ya ce muguwar rawar da jam’iyyun biyu suka taka a tsawon waɗannan shekaru ta nuna ƙarara cewa babu buƙatar a sake yin amanna da su a kan cewa za ta sauya zani idan aka sake ba su wata dama a nan gaba.

Ya ce: “APC da PDP sun yi [mulki] duk mun gani, ba gyara suke nufi ba. Idan ka dubi yaƙi da cin hanci da rashawar nan, duk mutanen da ake cewa barayi ne za a hukunta su saboda sun yi sata a karkashin PDP, yanzu sun lallaba sun koma APC, kuma shiru kake ji, don haka ne ni tuni na yi rijista da PRP na zama dan jam’iyya don duba ta yadda zan taimaka wa Najeriya”.

Jega ya ce ”shi ya sa mu muke ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a samar da wata dirka da duk mutumin kirki zai koma cikinta, domin bayar da tasa gudunmawar wajen kawo gyara a Najeriya”.

”A halin da ake ciki ka da mutum ya ce don yana malamin makaranta shi ke nan a zauna a sa ido, a bar maɓarnata a cikin jama’a su mamaye iko, don haka tun da maɓarnatan nan sun tare komai, har ta kai ga ko da kai mutumin kirki ne idan kana cikin jam’iyyunsu ba za ka iya tsinana komai ba, to ya kamata a samu wata tunga daban da za ta tara mutanen kirki,” in ji shi.

A cewar malamin jami’ar ”Tun 1979 nake malamin jami’a, shekaru 40 ke nan yanzu, don haka abun da na karanta da wanda na lura da shi a yayin da nake shugabantar hukumar zabe ta INEC, a gaskiya yadda na ga ‘yan siyasarmu na tafiyar da lamarin zabe da kuma yadda suke wakilci idan an zabe su, to gaskiya akwai abun tsoro.”

Tsohon shugaban na INEC ya kara da cewa rashin shugabanci na gari ne ya haifar da dukkan matsalolin da Najeriya ke fama da su, har ta kai ga wasu na neman a raba kasar a halin da ake ciki.

[ad_2]

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...