APC na dari-dari kan amfani da na’ura a lokacin zabe

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, a Najeriya Sanata Abdullahi Adamu ya nuna damuwa a kan shirin da hukumar zaɓe ke yi na aiki da na’urar tantance masu zaɓe da aika sakamako ta intanet da ake kira BVAS a babban zaɓen da ke tafe.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 93 a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya.

Shugaban Jam’iyyar ta APC ya ce yana shakkar ko bullo da tsarin amfani da na’aurar ta BVAS zai samar da kyakkyawan sakamako ga al’ummar kasar baki daya a zaben 2023.

A cewarsa Najeriya ba ta shirya amfani da wannan fasaha a lokacin zabe ba amma kuma ya ce idan za a yi to ya zama wajibi ga hukumar zabe ta tabbatar wa ‘yan Najeriya ta shirya dari bisa dari don ta gamsar da kowa da kowa.

Bala Ibrahim shi ne Darakatan yada labaran Jam’iyyar ya shaida wa BBC cewa damuwa shugaban jam’iyyar ya nuna a kan tasirin naurar wajen samar da sahinin zabe : “ Damuwa ce ga niyya ko kuma ganin an yi adalci ga kowa da kowa.”

“ Akwai wasu wurare wadanda a halin da ake ciki yanzu naurar ba ta aiki, wannan waya ta hannu akwai inda ba ta aiki.”

Sanata Abdullahi Adamu ya ce akwai ƙalubale sosai da ya shafi rashin wutar lantarki da rashin layukan intanet a yankunan karkara wanda idan ba a shawo kansa ba, zai yi wuya na’urar ta yi tasiri.

“ Har yanzu gwamnati na kokarin ganin cewa ta shawo kan wannan matsalar ta karanci wutar lantarki kuma wannan naurar da za a yi amfani da ita tana amfani da batir ne kuma a baya an sha kuka da cewa wasu baturan sun mutu a wasu wuraren kuma an kasa yin caji saboda rashin wuta” in ji shi.

Sai dai tun farko hukumar zabe ta ce naurar ta BVAS za ta taimaka matuka wajen dakile ayyukan masu magudin zabe kuma wasu sun yi zargin cewa jam’iyyar na neman kafa ne ta yin aringizo a lokacin zabe.

Sai dai zargi ne da darakatan yada labaran jam’iyyar Bala Ibrahin ya musanta :

“ Wannan tsari na amfani da naura jam’iyyar APC ce a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari aka fito da wannan tsarin, ita ce ta yi uwa ta yi makarbiyya wajen ganin wannan doka ta samu wucewa a majalisa”

Sai dai alamu sun nuna cewa da wuya hukumar zabe ta sauya matsayinta wajen aiki da wannan na’ura saboda a baya-baya nan ta ce babu gudu babu ja da baya wajen aiki da wannan naura.

Ita ma jam’iyyar APC ta ce tana son a yi amfani da naurar ta BVAS amma tana son a kara gyara abin ta yadda kowa zai ji dadinsa kuma wadanda za su sha kaye a zaben za su san cewa sun fadi ne a zabe mai sahihanci

More News

Ƴan bindiga sun buɗe wuta kan motar kulob ɗin Sunshine Stars

Ƴan wasa da kuma jagororin kungiya ne suka jikkata a wani hari da ƴan bindiga suka kai kan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Sunshine...

Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 5 tare da lalata sansaninsu 4 a Borno

Sojojin rundunar kasa da kasa dake samar da tsaro a yankin tafkin Chadi sun kashe mayaƙa 6 na ƙungiyar ƴan ta'adda ta ISWAP...

Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje da Ta’aziyya Jihar Kaduna

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje da ta'aziyya jihar Kaduna na mutanen da harin jirgin sojoji ya kashe a ƙauyen Tudun...

Tudun Biri:An gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya

Masu zanga-zanga a ranar Laraba sun tsinkayi ginin majalisar dokokin tarayya dake Abuja kan kisan da jirgin sojoji ya yiwa fararen hula a Kaduna...