Ana murnar gano man fetur da gas a Bauchi

NNPC


An dade da gano akwai albarkatun man fetur da iskar gas a jihar ta Bauchi

Al’ummomi musamman a arewacin Nijeriya na ci gaba da murna da mayar da martani tun bayan sanarwar da kamfanin samar da man fetur na kasar NNPC ya bayar cewa an gano man fetur da iskar gas a kogin Kolmani.

A farkon watan Fabrairun bana, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin fara tonon rijiyoyin mai a yankin da ya hada da jihar Bauchi da Gombe da Yobe gami da Adamawa.

Wata sanarwa da kamfanin NNPC ya fitar a karshen mako ta ce suna ci gaba da aiki a Kogin Kolmani don tabbatar da ko yawan man fetur d’in ya kai adadin da za a iya cinikayyarsa.

An shafe tsawon shekaru, ana fafutukar ganin hako man din da ake cewa akwai shi jibge a wasu sassan arewa maso gabashin Najeriya.

  • An samu man fetur a Bauchi – NNPC
  • ‘Barayin fetur na sa kamfanin Shell asarar $560,000 kullum a Najeriya’

Sanata Salisu Ibrahim Musa Matori na daya daga cikin dattijan jihar Bauchi, wadanda suka dade suna ta fadi-tashin ganin cikar wannan buri, kuma ya shaidawa BBC cewa sama da shekaru 20 da suka gabata aka fara batun,

”To amma gwamnatin wancan lokacin ba ta maida hankali akai ba, watakil saboda ba ya cikin ajandarta. Sai bayan zuwan wannan gwamnati na APC ne aka sake matsa kai mi kuma Allah cikin ikonsa ta tabbata akwai mai a kogin Kolmani”, inji Matori.

Matori ya kara da cewa” Alfanun da za a ci na samun mai da iskar gas zai kasance ya raba matasa da zaman kashe wando, da samawa gwamnati kudaden shiga wanda muke fatan Najeriya baki daya za ta amfana da shi”.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...