Ana fargabar mutuwar mutane da dama a hatsarin jirgin ruwa a jihar Niger

Akalla kusan mutane 100 ake fargabar sun mutu a wani Hatsarin jirgin ruwa a jihar Niger.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger ta ce hatsarin ya faru ne a karamar hukumar Borgu ta jihar ranar Litinin da rana.

Abdullahi Baba Arah darakta janar na hukumar ya ce jirgin ya taso ne daga kauyen Dugga Mashaya a mazabar Dugga inda ya nufi kasuwar Wara dake jihar Kebbi.

Baba-Arah ya ce jirgin na ɗauke sa fasinja da aka ƙiyasta cewa za su kai 100 tare da kayayyaki da suka haɗa da hatsi da kuma wasu kayayyakin.

A cewarsa hukumar bata iya gano yawan mutanen da suka mutu ba ko kuma suka tsira a hatsarin.

Ya kara da cewa ana cigaba da aikin nema da kuma ceto mutanen tsakanin ma’aikatan hukumar dana karamar hukumar da kuma mutanen yankin da suka ƙware a yin iyo.

More from this stream

Recomended