An yi Jana’izar dan majalisar Lagos da ya mutu a Jos wurin yakin neman zaben APC

0

An gudanar sallar jana’izar,Abdul-Sobur Olayiwola Olawale dan majalisar dokokin jihar Lagos wanda ya mutu a Jos a wurin yakin neman zaben Bola Ahmad Tinubu.

Dan majalisar ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu nan take.

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu da kuma shugaban majalisar dokokin jihar, Mudashiru Obasa na daga cikin wadanda suka halarci jana’izar marigayin.