A ranar Lahadi ne aka yi bikin ƙaddamar da fara zirga-zirgar jiragen sama na kamfanin Rano Air.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya jagoranci bikin da ya gudana a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano dake Kano.
Alhaji Auwal Abdullahi Rano shugaban rukunin kamfanin AA Rano shi ne mamallaki kuma shugaban kamfanin jiragen na Rano Air.



