An yanke wa Musulmi 29 hukuncin kisa saboda rikicin limancin sallar Idi

An kone motocin 'yan sanda a rikicin da aka yi a inda za a yi sallar Idin a filin wasa na Martyrs' Stadium

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
An kone motocin ‘yan sanda a rikicin da aka yi a inda za a yi sallar Idin a filin wasa na Martyrs’ Stadium

An yanke wa Musulmi ashirin da tara hukuncin kisa, saboda rikici kan limancin sallar Idi a Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dan sanda daya, da jikkata gommai.

Rikicin ya tashi ne ranar Alhamis a babban birnin kasar, Kinshasa tsakanin kungiyoyi biyu na Musulmi a kan sabani dangane da wanda zai jagoranci sallar Idi.

An kama mutanen arba’in da tara ne da aka gurfanar gaban shari’a, a Kinshasha, babban birnin kasar, a wajen filin wasa na Martyrs’ Stadium, inda nan ne za a yi sallar Idin bayan kammala azumin watan Ramadan, inda a nan ne aka yi rikicin.

An dai rika nuna zaman shari’ar kai tsaye ta talabijin duk tsawon dare.

Sai dai kasancewar yanzu ba a aiwatar da hukuncin kisa a kasar ta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo, a madadin hakan mutanen za su yi zaman gidan yari ne na tsawon shekaru.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Daya daga cikin ‘yan sandan da aka ji wa rauni

Hukumomi sun ce yayin tashin hankalin, wanda aka samu tsakanin bangarori biyu na Musulmi da ke da sabani da juna, kan wanda zai jagoranci sallar Idin ta karshen azumi, an kashe dan sanda daya, wasu gommai sun samu raunuka, wasu kuma da daman a cikin mawuyacin hali sakamakon raunin da suka ji.

Daman akwai dadden sabani kan neman shugabancin kungiyar al’ummar Musulmi a wannan yanki na Jamhuriyar Dumokuradiyyar ta Kongo, tsakanin wadannan kungiyoyi biyu da ke da sabani.

Tun da farko dai sai da jagororin kungiyoyin biyu suka ba wa hukumomi babban birnin, Kinsasha tabbacin yin sallar Idin da kuma bikin Sallar tare cikin kwanciyar hankali, amma kuma aka samu tashin-tashinar

A lokacin fadan ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsasan roba wajen tarwatsa mutanen da suka hallara domin sallar Idin, bayan da rikicin ya kaure.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Ana yin sallar Idin lami lafiya kamar nan yadda aka yi a 2017

Mutane arba’in da daya aka kama a wurin rikicin a ranar ta Alhamis, washe gari, Juma’a kuma aka gurfanar da su gaban shari’a.

Talatin da daya an same su da laifi, inda aka yanke wa 29, hukuncin kisa, biyu kuma daurin gidan yari na shekara biyar.

Ana dai ganin yadda aka yi sharia’r cikin sauri haka, akwai yuwuwar shakku ko tababa ta adalci kan shari’ar.

Kusan kashi goma cikin dari na al’ummar kasar ta Kongo (Kinshasa) musulmi ne kuma yawanci suna yankin gabashin kasar ne

Sai dai birnin Kinshasa wanda ke bangaren yamma na katafirayar kasar da ke yankin tsakiyar Afirka, shi ma yana da tarin Musulmi da ke bikin sallah a karshen azumin watan Ramadhana, da ake yi a manyan titunan birnin da filaye ko wuraen haduwar jama’a na gwamnati.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...