Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na ɗaurarrun da suka tsere da gidan gyaran hali da tarbiyya na Suleja dake jihar Niger.
A ranar 24 ga watan Afrilu wani mamakon ruwan sama ya rushe wani sashe na katangar gidan gyaran hali na Suleja har ta kai ga ɗaurarru 118 sun tsere.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya ɗora alhakin rushewar katangar kan tsufa da tayi.
Inda ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da kare faruwar haka anan gaba.
Ƴan kwanakin da suka wuce, Abubakar Umar mai magana da yawun hukumar ta NCoS ya ce an samu nasarar kama 23 daga cikin fursunonin da suka tsere.
Ya zuwa ranar 15 ga watan Yuni hukumar ta wallafa sunayen mutanen da suka tsere a shafin intanet na hukumar.
Sunayen da aka wallafa sun haɗa da Ogbonna Kingsley, Auwal Mohammed, Mustapha Ibrahim, Suleiman Sani, Raphael Kelly, Abdullahi Babangida, Idris Bashir, Umar Mustapha, Ayuba Obedience, da Lamido Gambo.
Sauran su ne Garba Fidelis, Mohammed Jibrin, Sylvester Allison, Albert Israel, Edoga Okwudili, Olaiya Stephen, Ibrahim Aminu, da Audo Usman.