An Tura Karin Yan sanda Zuwa Kan Hanyar Abuja-Kaduna

Kayode Egbetokun babban sifetan yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin tura karin jami’an tsaro da kuma kayan aiki kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Hanyar ta Kaduna zuwa Abuja ta kasance wata cibiyar da yan fashi daji ke kisa tare da yin garkuwa da mutane.

Sama da matafiya 80 ne aka yi garkuwa da su akan hanyar tsakanin ranakun 4 zuwa 7 ga watan Janairun 2024.

Mutane huɗu aka kashe a jerin hare-haren da yan fashin dajin suka kai a kan hanyar.

A wata sanarwa ranar Alhamis, Muyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar yan sanda ta kasa ya ce babban sifetan ya umarci Ede Ayuba Ekpeji mataimakin babban sifetan yan sanda mai kula da ayyukan yau da kullum da ya tabbatar da anbi umarnin sau da kafa na tura karin jami’an tsaron.

Adejobi ya ce Egbetokun ya yi kira da a samu hadin kai tsakanin jami’an tsaro da kuma al’ummar garuruwan da harin ke shafa.

More from this stream

Recomended