An samu wata mace mai dauke da coronavirus a Najeriya

Mutane na ci gaba da daukar matakan kariya a kasar don kauce wa kamuwa da coronavirus

Mutane na ci gaba da daukar matakan kariya a kasar don kauce wa kamuwa da coronavirus

An samu wata mace dauke da coronavirus a Najeriya, wadda ta zama ta uku da aka samu da cutar a kasar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Lagos ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter a ranar Talata.

Matar mai shekara 30 ta dawo ne daga Birtaniya ranar 13 ga watan Maris – wadda bayan isowarta sai ta killace kanta, inda ta dinga ganin alamun cutar.

Tuni Ma’aikatar Lafiya ta jihar Legas ta yi kira ga duk fasinjojin da suka shigo Najeriya da jirgin British Airways 75, a ranar Juma’a 13 ga watan Maris, da su zauna a gidajensu har tsawon kwana 14.

An yi mata gwaji aka kuma tabbatar ta kamu da Covid-19, inda a halin yanzu take babban Asibitin Gwamnati na jihar da ke Mainland.

Yanzu kasar ta samu mutum uku kenan masu dauke da cutar tun farkon bullarta a Najeriyar ranar 28 ga watan Fabrairun 2020.

Nan gaba a yau ne ake sa ran hukumomin Najeriya za su bayyana wasu matakai kan batun shigowa kasar da kuma shawarwari kan taruwar jama’a.

Dukkan masu cutar uku da aka samu a kasar daga jihar Legas ne.

Matar ita ce mace ta farko da ta kamu a kasar. Coronavirus ta kashe a kalla mutum 7,174 a duniya zuwa yau.

Sannan mutum 182,726 ne suke dauke da Covid-19 a kasashe fiye da 150.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...