Gobara ta sake tashi a kasuwar Gamboru da ke kusa da unguwar Kwastam a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Idan ba a manta ba dai, a ranakun 18 ga Maris, 2023 da 13 ga Nuwamba, 2023, gobara ta kone kasuwar da aka ce ita ce babbar kasuwar kayan gwari a Maiduguri.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno, Alhaji Usman Tar, ya ce gobarar ta tashi ne a Layin Yan Katako da kuma wajen kasuwar.
Malam Tar, a cikin wata sanarwa, ya ce lamarin wanda ya faru a ranar Laraba da misalin karfe 10 na dare, jami’an hukumar kashe gobara ne suka yi nasarar kashe ta.