An sako mutane 11 da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Yan bindiga sun sako mutanee 11 daga cikin 61 da suka yi garkuwa da su bayan harin da suka kai kan jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna.

A ranar 28 ga watan Maris ne maharan dauke da muggan makamai suka kai hari kan jirgin inda suka kashe mutane 9 tare da jikkata 28 kana suka yi awon gaba da 63.

Mutanen da aka sako sun hada da mata shida da maza biyar a cewar Alhaji Tukur Mamu mawallafin jaridar Desert Herald dake Kaduna wanda yake jagorantar tattaunawa da yan bindigar.

Wani daga cikin iyalan wata da aka saka mai suna Abdullahi Sani ya tabbatar da sakin yar uwar ta sa cikin wani sako da ya wallafa a Facebook ranar Asabar.

Mamu ya ce an sako mazan biyar ne saboda rashin koshin lafiya yayin da matan suke cikin wadanda suke da rauni.

Amina Baaba Mohammed,Rashida Yusuf Buda,Jessy John,Hanna Adewole da Amina Jibril na daga cikin matan da aka saka.

Mazan sun hada da Najib Mohammed Dahiru, Hassan Aliyu, Peace A. Boy, Danjuma Sa’idu da kuma Gaius Gambo.

More from this stream

Recomended