An kona ofishin INEC a Enugu

Wasu mutane da ba a san ko suwaye ba sun cinna wuta a ofishin hukumar zabe ta INEC dake karamar hukumar Igboeze North a jihar Enugu.

An ka hari ofishin hukumar zaɓen ne da misalin karfe 11: 48 na daren ranar Lahadi.

Kwamishinan zabe na jihar Enugu,Emeka Ononamadu ya bayyana cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba a harin wutar ta kone a akwatunan zabe 748 da kuma akwakun kada kuri’a 240.

Duk da cewa babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin sai dai yayi kama da irin wanda ƴaƴan kungiyar IPOB suke kai wa a yankin kudu maso gabas.

More from this stream

Recomended