An Kawo Karshen Shari’ar Jamhuriyar Nijar da Kamfanin Africard

[ad_1]

A ci gaba da neman hanyoyin kawo karshen shara’ar da bangarorin suka shafe shekaru suna tafkawa a gaban kotunan Amurka da Faransa da Faransa sakamakon rashin fahimtar da ta biyo bayan matakin soke wata kwangilar buga fasfo da kamfanin na kasar Birtaniya ke zargin gwamnatin Nijar ta dauka ba akan ka’ida ba.

A farkon watan satumban dake tafe ne ya kamata kotun daukaka kara ta birnin Paris ta bayyana hukuncin da za ta yanke a shara’ar da aka shafe shekaru kusan biyar ana tafkawa game da matakin soke kwangilar da kamfanin Africad da kasar Nijar tayi. Sai dai kuma kotun ta bukaci wadanan bangarori su yi sulhu da juna.

Sakamakon sulhun da aka samu kotun ta bukaci kasar Nijar ta biya miliyan 5000 na CFA domin ragewa Africard asara a maimakon miliyan 24,000 da ya nuna bukatarsu a can baya.

Sannan kamfanin ya amince ya saki kadarorin gwamnatin Nijar da ya kama a ketare da suka hada da gidaje da kudaden ajiya a Banki inji tawagar lauyoyin gwamnati.

Sakamakon wannan takaddama hukumomin Nijar a shekarar 2017 sun kori wasu manyan jami’anta daga aiki cikinsu har da sakataren gwamnati Ganduou Zakara, saboda zarginsu da sakaci akan aiki sai dai wasu ‘yan kasar na ganin da alama har yanzu jami’an kasar ba su koyi darasi ba.

Gwamnatin rikon kwarya ta Gen Salou Djibo ce ta rattaba hannu akan yarjejeniyar bayar da kwangilar buga Fasfo ga kamfanin Africard a shekarar 2011, to amma gwamnatin Issouhou Mahamadou ta soke wannan aiki saboda a cewarta akwai wasu matsalolin da talakkawa ke bukatar hukumomi su magance cikin hamzari a wancan laokacin, a maimakon batun buga Fasfo matakin da kamfanin na kasar Birtaniya yace ba zai lamunta da shi ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

[ad_2]

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...