An kashe yan sanda 3 da yan bijilante 5 a Kogi

Akalla Yan sanda uku da kuma yan bijilante 5 yan bindiga suka kashe a Ajaokuta dake jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne bayan da mazauna yankin suka lura zirga-zirgar wasu mutane da basu yarda da su ba a wajen caji ofis din Yan sanda na Ajaokuta.

Mai bayar da shawara kan harkar tsaro na jihar Kogi, Kwamanda Jerry Omadara ya ce yan sandan uku da kuma yan bijilante 5 sun mutu sanadiyar harin kwanton bauna da suka maharan suka yi musu.

Ya ce bayanan sirri da DPO yankin ya samu na cewa yan bindiga sun mamaye wata gona kuma suna aikata ba dai-dai ba hakan yasa ya tattara jami’ansa da kuma wasu yan bindijilante domin zuwa wurin.

More from this stream

Recomended