An kashe mutane 42 a jihar Zamfara

[ad_1]








Barayi dake ɗauke da makamai sun kashe akalla mutane 42 lokacin da suka kaddamar da hare-hare kan wasu ƙauyuka 18 dake lardukan Mashema, Kwashabawa da kuma Birane dake karamar hukumar Zurmi ta jihar a ranar Juma’a.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu za su iya kai wa 100 domin ba a inda wasu mutanen suka shiga ba.

Jaridar Daily Nigerin ta gano cewa maharan sun kuma kona yawancin gidajen dake ƙauyukan da suka kai harin.

Wani da ya tsira daga harin, Lawali Mashema ya ce dubban mazauna kauyukan da harin ya raba da gidajensu sun gudu zuwa garin Zurmi dake da tazarar kilomita 50 daga garin su.

Wasu da dama kuma na gudun hijira a jihar Katsina da kuma jamhuriyar Nijar.




[ad_2]

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...