An Kashe Mutane 3 A Wani Rikicin Kabilanci A Cross Rives

Mutane 3 ne aka kashe a wani rikicin kabilanci a  Nnaorokpa dake ƙaramar hukumar Nta Ikom ta jihar Cross River.

Mutanen da suka mutu a rikicin sun haɗa  da Rejoice Nton,wata ɗaliba mai shekaru 10, da Mariam Akanya Mfono mai shekaru 20 sai kuma mutum na uku wacce ta kawo ziyara ne yankin.

Mazauna garin sun ce rikici tsakanin Nnaorokpa dake ƙaramar hukumar Nta Ikom da kuma Ofunokpan a ƙaramar hukumar Obubra  ba sabon abu ne domin an ɗauki tsawon shekaru 30 ana yi kuma ya lakume rayukan mutane da dama.

Suka ce rikicin na cigaba faruwa duk da koƙarin da gwamnatin jihar take yi na sasanta rikicin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Irene Ugbo ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce tuni jami’an tsaron suka shawo kan lamarin.

More from this stream

Recomended