An kama wasu mutane dake tayar da rikici a ƙaramar hukumar Mangu

Jami’an rundunar Operation Safe Haven dake samar da tsaro a jihar Filato sun samu nasarar kama wasu mutane da suke zargi da haddasa rikici a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

A wata sanarwa jami’in hulda da kafafen yaÉ—a labarai na rundunar, Oya James ya ce an samu kai mummunan hari da kuma barnatar dukiya daga wasu matasa a Kerang dake karamar hukumar ta Mangu.

Ya Æ™ara da cewa matasan ba iya barnar kadai suka tsaya ba har sai da ta kai sun kai hari kan jami’an sojojin dake aikin tabbatar da bin dokar hana fita da aka saka yankin.

Sanarwar ta kara da cewa an samu makamai da dama daga hannun matasan da aka kama.

More News

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...

NFF ta naÉ—a Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...