‘An kama masu laifi sama da 2000 cikin shekara 1 a Bauchi’

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce an kama mutane akalla 2,077 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a ciki da wajen jihar a cikin shekara guda, tsakanin Yuli 2023 zuwa Yuli 2024.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce an samu wannan nasarar ne a karkashin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi, CP Auwal Musa, wanda ya fara aiki a ranar 6 ga Yuli 2023.

Wakil ya nuna cewa “Jihar Bauchi na daya daga cikin Jihohin da ke yankin Arewa maso Gabas da ke fuskantar kalubalen tsaro da dama kamar su garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, satar shanu, ‘yan daba, fyade da sauran munanan laifuka.”

Ya ba da misali da wuraren da ake tafka laifuka daban-daban da suka hada da dajin Lame Burra a karamar hukumar Ningi, dajin Balmo a cikin Ganjuwa L.G.A, dajin Yuda da dajin Mundu a dajin Toro L.G.A, Dajin Madam da dajin Yankari a cikin Alkaleri L.G.A, inda ya bayyana cewa yankunan sun ba da mafaka ga masu aikata laifuka.

A cewar Wakil, dangane da daukar mataki a matsayin kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi na 45, ya samar da matakan da suka dace ta hanyar hada kai da masu ruwa da tsaki da sauran hukumomin tsaro;  kungiyoyin ‘yan banga; cibiyoyin addini/na al’ada da matasa.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...