An kai sabon hari a Jihar Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Nasarawa da ke garin Maru, hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Da sanyin safiyar Juma’a ne maharan suka mamaye yankin inda suka yi ta harbe-harbe don tsorata mazauna yankin.

An ce sun isa ƙaramar hukumar ne da yawansu ɗauke da makamai.

Hukumomin ‘yan sanda a jihar har yanzu ba su tabbatar da sabon harin ba.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara Yazid Abubakar bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Sai dai wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya shaida wa wani gidan talabijin cewa Dakarun Operation Hadarin Daji sun yi gaggawar amsa kiran da suka yi musu.

An yi musayar wuta da aka kwashe sama da awanni biyu ana yi.

More from this stream

Recomended