An jibge sojoji da jirgin yaki a Sokoto do Zamfara

Sojojin za su yi yaki ne da 'yan fashi a Sokoto da Zamfara

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Air Force

Image caption

Sojojin za su yi yaki ne da ‘yan fashi a Sokoto da Zamfara

An tura dakarun sojin saman Najeriya da jirgin yaki da makamai zuwa Sokoto domin yaki da ‘yan fashi da masu garkuwa mutane.

Sanarwa da kakakin rundunar sojin sama Ibikunle Daramola ya tura wa manema labarai, ta ce an tura dakarun ne tare da jirgin yaki domin taimakawa rundunar Operation Diran Mikiya da ke yaki da ‘yan bindiga tsakanin kan iyakar Sokoto da Zamfara da Katsina

Tuni sojojin suka isa Sokoto a ranar Lahadi domin soma yaki da ‘yan fashi da suka addabi yankin na arewa maso yammacin Najeriya.

  • An kama ‘yan bindigar da suka sace tagwaye a Zamfara
  • ‘Yan sa-kai na ‘kashe mutane a kasuwannin Zamfara’

Babban kwamandan sojin sama a Sokoto Air Vice Marshal Oladayo Amao da ya tarbi sojojin, ya bukaci su nuna kwarewa ga aikin da aka turo su na tabbatar da tsaron al’umma da kuma yakar ‘yan fashi.

Sanarwar ta kuma ce za a inganta filin jirgin Sultan Abubakar III a Sokoto da dukkanin abubuwan da suka wajaba domin kaddamar da hari ta sama daga tashar jirgin saman.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Air Force

[ad_2]

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...