
Hukumar dake lura da filayen jiragen sama ta Najeriya FAAN ta sanar da matafiya ta filayen jiragen sama cewa daga yanzu ta haramta amfani da jakar zuba kaya ta Ghana Must Go.
Hukumar ta ce dokar za tafi aiki musamman ga matafiya masu zuwa kasashen waje.
Jakar ta Ghana Must Go na da farin jini musamman ga matafiya a Najeriya.
Hukumar ta FAAN ta bayyana cewa ta hana amfani da jakar ne saboda yadda take lalata na’urar da ake ɗora jakunkuna ya zuwa cikin jirgi inda hakan yake jawo gagarumar asara ga kamfanonin jiragen sama.
Tuni wasu daga cikin kamfanonin jiragen sama suka fara sanar da abokan huldar su cewa a yanzu baza su amince fasinja ya zo da kaya a cikin jakar ta Ghana Must Go ba.