An hallaka mutane akalla 29 a Burkina Faso | BBC news

Ofishin jakadancin Faransa a Ouagadougou

Hakkin mallakar hoto
AFP

Hukumomi a arewacin Burkina Faso sun ce an kashe mutane akalla 29 a wasu hare-hare daban guda biyu da ake zargin Musulmi masu ikirarin Jihadi ne suka kai.

A wata sanarwa, gwamnatin Burkina Fason ta ce mutane akalla 15 ne suka mutu, shida kuma suka samu raunuka, lokacin da wata babbar mota ta taka wata nakiya ko bam a lardin Sanmatenga.

Sannan kuma a wani hari da aka kai kan jerin gwanon wasu motoci da ke dauke da kayan abinci da za a kai wa ‘yan gudun hijira, an kashe farar hula akalla goma in ji hukumomi.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An kara tsaro a yankin

Gwamnatin Burkina Fason ta ce tuni an tura karin sojoji yankin domin kai dauki.

Kasar dai ta fara fama da hare-haren masu ikirarin Jihadi, da suka bazu zuwa can daga Mali, zuwa Arewaci, sannan kuma zuwa gabashin Burkina Fason a 2015.

Tun daga sannan da abin ya fara an yi kiyashin hallaka mutane sama da 500 a kasar ta yammacin Afirka.

Daga nan kasar ta Burkina Faso ta kasance daga kasashen katafaren yankin Sahel da ke fama da tashin hankali na kungiyoyin Musulmi masu ikirarrin Jihadi a yankin.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Kusan mutane 100,000 ne tashin hankali ya raba da muhallansu a Burkina Faso

Ita tare da makwabtanta na yankin Nijar, Chadi, da Mauritania da kuma Mali suka hadu suka samar da dakarun kungiyar da ake kira, G5 Sahel, domin kawar da barazanar mayakan.

A watan Janairu Firaministan kasar, PM Paul Kaba Thieba ya sauka daga aiki sakamakon matsin-lamba a kan karin sace-sacen jama’a da hare-haren masu ikirarin Jihadin, aka kuma maye gurbinsa da Christophe Joseph Marie Dabiré.

Tsohuwar uwar-gijiyar yankin ta mulkin mallaka, wato Faransa, tana da dakaru 4,500 a kasashe hudu, domin yakar masu tayar da kayar bayan Musulmi.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...