An girke sojoji 300 a biranen Brazil

Brazil
Image caption

‘Yan kasuwa sun rufe shagunansu bayan an fara kone wasu daga ciki

Hukumomi a kasar Brazil sun girke daruruwan sojoji a arewacin jihar Ceara bayan barkewar tarzomar da gungun masu safarar miyagun kwayoyi suka tada.

Kusan sojoji 300 aka girke a birnin na Fortaleza dan tabbatar da tsaro, wasu daga ciki kuma za su sanya ido kan gine-ginen gwamnati saboda kaucewa abinda ya faru a jihar Ceara.

Tuni ‘yn kasuwa suka rufe shaguna bayan da aka fara kona wasu daga ciki harkokin sufuri sun tsaya cak, inda su ma motocin Bus-Bus ba su tsira da aka cinna musu wuta a daya daga cikin toshoshin da suke tsayawa.

Ma’aikatar shari’a ce dai ta dauki matakin na girke jami’an sojin, bayan kwashe mako guda gungun kungiyoyin safarar muggan kwayoyi sun tda tarzoma saboda daukar sabbin matakan da sabuwar gwamntin shugaba Jair Bolsonaro ta dauka a gidajen kason ksar wadanda ywancin kungiyoyin ne ke tafiyar da su a baya.

Hukumomin gidajen kason sun far daukar mtkan toshe hanyoyin sadarwa a cikinsu, ya yin da suka ki amincewa da al’dar nan ta rabawa fursunoni wuraren zama a duk lokacin da masu safarar kwayoyin suka bukata.

Wata kididdig da hukumar gidajen kaso ta duniya ta fitar a shekarar da ta gabata, ta ayyana Brazil a matsayin kasa ta 3 da tafi yawan tsare masu laifi a gidajen kaso, inda ake tsare da sama da mutane Dubu dari bakwai, ya yin da kasr Amirka ke ce ta frko sai kuma China.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadn byan shan rantsuwar kama da aikin shugaba Bolsonaro, wanda ak zaba da alkwarin zai magance cin kare babu babbak da kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu safarar kwaya ke yi a kasar.

Da magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yi wa kasar katutu, wand tuni sabon ministan sharia’r Brazil Sergio Moro ya fara kaddamarw da kai wa lakabi da Operation Car Wash.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...