An gargadi Twitter kan sabbin dokokinta

Tarayyar Turai ta gargadi mai kamfanin Twitter Elon Musk cewa dole ne ya tashi tsaye wajen ganin kamfanin na bin sabbin dokokin kungiyar a kan labaran karya ko kuma ta haramta shafin.

Kwamishinan kungiyar Thierry Breton ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da Mista Musk ranar Laraba.

Ya ce dole ne shafin na sada zumunta da muhawara ya yi gyara a kan batutuwan da suka shafi sakonnin da ake rubutawa da labaran karya da kuma tallace-tallacen da ake nufa da wasu masu amfani da shafin.

Wannan mataki ya biyo bayan shirin fara aiwatar da sabbin dokokin da Tarayyar Turan ta bullo da su.

A farkon wannan shekarar ne Turai ta bullo da dokokin na shafukan intanet, wadanda ke ganin kusan su ne wani babban garambawul da ta yi a cikin gomman shekaru, inda ta sanya matakan hana kamfanonin intanet saba ka’idoji.

A shekara mai kamawa ne ake ganin manyan kamfanonin intanet za su fara aiki da sabbin dokokin.

Duk kamfanin shafin da aka samu da saba dokar, za a ci tararsa kashi 6 cikin dari na cinikinsa na shekara ko kuma a haramta masa aiki idan aka same shi da karya dokokin a kai-a kai.

A wata sanarwa da ya fitar bayan ganawar tasu, Mista Breton ya ce ya yi maraba da tabbacin da Mista Musk ya ba shi cewa kamfanin Twitter zai kiyaye da dokokin.

Kwamishinan na Tarayyar Turai ya ce, a shekara mai zuwa 2023 Tarayyar za ta gudanar da binciken game da bin dokokin da kuma tasirinsu.

Tun bayan da ya sayi kamfanin a kan dala biliyan 44 a watan da ya gabata Mista Musk ya sallami dubban ma’aikata, sannan kuma ya mayar da masu amfani da shafin da aka dakatar a da kamar su tsohon shugaban Amurka Donald Trump, sanna kuma ya hana tlasta wasu dokoki.

Kamar dokokin hana sanya lamabaran da za su batar da mutane game da cutar korona.

Matakan sun tayar wa da wasu kungiyoyin kare hakkin dan’Adam wadanda suka zargi hamshakin attajirin da daukar matakan da za su kara angiza yin kalamai na haddasa tsana da labaran karya da kuma na cin zarafi.

Wasu kamfanonin da suke tallata hajarsu a shafin sun dakatar da kasha kudadensu saboda fargabar da suke yi cewa kamfanin zai iya samun kansa a cikin wani mawuyacin hali, kasancewar ya dogara ne a kan tallace-tallacen wajen samun yawancin kudadensa.

A wata sanarwa da ya sanya ranar Laraba kamfanin na Twitter ya ce bai sauya komai daga cikin manufofi da tsare-tsarensa ba, amma dai yana nazari tare da gwaji a kokarin da y ace yana yin a inganta ayyukansa dokin hana sab awa dokokinsa, tare da bayar da ‘yancin fadin albarkacin baki, amma ba ‘yancin cimma manufa ba.

Kamfanin ya kara da cewa kwararru kuma jajirtattun ma’aikatansa na aiki kai da fata wajen tabbatar da hakan, da kuma tsarinsa na gano duk wani abu na cin zarafi ko saba ka’ida domin kawar da su.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...