An fasa auren budurwa saboda yaɗa bidiyon tsiraicinta a Sokoto

yarinya a cikin duhu

Hukumar Hizbah a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da kama wasu matasa su uku bisa zarginsu da yaɗa bidiyon wata yarinya da ɗaya daga cikinsu ya yi lalata da ita.

Bayanai sun nuna an saka ranar auren yarinyar a watan gobe, amma sai wanda zai aure ta ya janye bayan da waɗannan matasan da ake zargi suka saki bidiyon a shafukan sadarwa.

Kwamandan hukumar Hisbah Dr. Adamu Bello Asarawa ya shaida wa BBC cewa mahaifiyar yarinyar ce ta kai musu ƙorafi inda ta ce tun a shekarar 2017 matasan suka lalata yarinyar tare da ɗaukar bidiyon.

Dr. Adamu ya ce ”Matashin ya yaudari yarinyar ne ya kai ta otel kuma ya ɗauki bidiyon tsiraicinta. Sai bayan da ta samu miji za ta yi aure sai kawai aka ga ya saki bidiyon.

”Mun binciki yaron ya kuma tabbatar mana cewa abin ya faru, zuwansu otel da abin da ya yi da ita, sannan mun kamo abokansa biyu da ya tura wa kuma su ma sun yi ikirarin cewa shi ya tura musu. Don haka duk wanda ya samu bidiyon daga baya to ta hanyar abokan nan biyu ya samu, ” a cewar kwamandan.

Me ya sa yaron ya ɗauki bidiyon?

Kwamandan hukumar Hisbah ya ce yaron bai bayar da wasu dalilai da suka sa ya ɗauki bidiyon tare ya yaɗawa ba.

”Ɓarna dai ta riga ta faru. Rashin tarbiyya ce irin ta yara. Ina ga ya yi hakan ne don cin zarafi da lalata mata rayuwa da kuma suna,” in ji Dr. Adamu.

Kwamandan ya ce sun tambayi yaron ko zai auri matashiyar ne tun da yanzu ya lalata maganar aurenta, ”sai ya ce min ba shi da niyyar hakan, ai ba zai iya aurenta ba don dama da niyyar yaudara ya je,” in ji shi.

Shekarun yaron 17 ita kuma yarinyar tana da 16 a lokacin da lamarin ya faru. A yanzu kuma yaron na da shekara 20 ita kuma 19 a cewar shugaban Hisbar.

”Dukkansu yara ne lokacin da abin ya faru don ba wanda ya kai 20.”

Me iyayen yarinyar suka ce?

A cewar mahaifiyar yariyar wadda yanzu aka ce shekarunta kimanin 20, babban wanda ake zargin ya yi lalata da ‘yar tata ne tun a shekara ta 2017 kuma ya nadi masha’ar ta wayar salula.

Ta ce ya ajiye bidiyon tsawon shekaru uku da nufin wata rana ya yi amfani da shi wajen bata sunanta idan yau da gobe ta halinta suka babe.

”Ni dai a cikin wata Yuni ina zaune yayata ta kira ni daga Legas tana ta slati ta ce ga wnace nan ta ganta a bidiyo tsirara ana ta yaɗawa. Sai na kira ƴar tawa na tamabaye ta, sai ta ce min ita ma yanzu take jin labari wajen wata ƴar makarantarsu.

”Sai na ce wa take zargi? Sai ta gaya min sunan yaron. Na ce ta ba ni nambarsa. Daga nan na je har gidan iyayensa, na tambayi yaron me ƴata ta yi masa a rayuwa da ya zaɓ yi mata wannan cin mutuncin.

”Sai ya ce ba abin da ta yi masa. Ga yarinya a bidiyon kamar wacce ta sha wani abu ta bugu. Duk wanda ya san tarbiyyar da na yi wa ƴata doole ya taya ni kuka wallahi.

”Daga nan sai mahaifiyar yaron ta kira babansa, ta ce ka zo ka ga abin da ɗanka ya aikata. Daga nan uban ya neme shi da ya nuna mana, sai kuwa yaron ya buɗe bidiyon muka gani.”

Uwar yarinyar ta ce bayan haka ne uban yaron ya nemi d aa taru a rufawa juna asiri, ”don a ganinsa hakan ba wani abu ba ne,” kamar yadda uwar ta ce.

”Sai ya ce min ai da a ce ciki ne da sai a shiga tashin hankali. Ni ko na ce wannan ma tashin hankali ne. Sai kawai ya ce na je dai kawai.

”Ni ko daga can sai na tafi Hizbah na kai ƙararsu. Da yanzu bikin ƴata 17 ga watan Oktoba ne, amma yaron ya ce ya fasa auren don shi suka fara aika wa bidiyon.”

Haka kuwa aka yi in ji rahotanni, bayan yarinya ta yanke shawarar yin aure da wani ba shi ba sai ya saki bidiyon a shafukan sada zumunta abin da ya sa wanda za ta auran ya ce ba da shi ba.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta

Wane hali yarinyar ke ciki?

Mahaifiyar wannan yarinya dai ta ce a yanzu haka yarinyar na cikin tsananin damuwa ta yadda ko abinci ba ta ci. ”Ba ta da aiki sai kuka dare da rana.

”A yanzu haka dole mu nemi inda za mu kai ta don ta samu kwanciyar hankali,” a cewar uwar.

Mahaifiyar yarinyar ta ce babban burinta shi ne a bi mata hakkin cin zarafin da aka yi wa ƴarta.

Wane hukunci za a yi wa yaron da abokansa?

Kwamandan Hisbah ya ce za a kai maganar gaban hukumar NAPTIP don ta duba ta ga dokokin da aka tanada kan ɓangaren abin da ya shafi ikirari na saduwa ga masu ƙananan shekaru.

”Su ne ke da hakkin hakan. Sai kuma mu kai hukumar tace bidiyo da fina-finai wato Censor Board don su ma su yi nasu aikin.

”Idan sun yi abin da ya dace daga nan kuma sai akai maganar kotu. Kuma abin d ya s za a haɗa da abokan biyu saboda su nasu laifin shi ne na yaɗa batsar da baɗalar,” a cewar Dr Adamu.

More News

Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban Riƙon Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam'iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam'iyar. Mai Shari'a  Peter Lifu shi...

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...