An Dawo Da ƴan Najeriya 108 Da Suka Maƙale A Ƙasar Libya

Ƴan Najeriya da basu gaza 108 da aka dawo su daga Libiya gwamnatin tarayya ta karɓa ta hannun hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA.

Waɗanda aka dawo dasu an ɗauko daga birnin Tripoli cikin jirgin kamfanin Al Buraq Air kirar Boeing 737-800 ya sauka a bangaren jirgin kaya na filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos da misalin karfe 05:55 na yamma.

Masu dowawar wanda kungiyar IMO ta majalisar dinkin duniya dake lura da yan gudun hijira ta taimaka musu wajen dawowa sun haɗa manyan mata 46 kananan yaran mata biyu da kuma jaririya ɗaya.

Sauran sun haɗa da maza manya 52 kananan yara 4 da kuma jarirai maza 4.

Da yake karɓar mutanen shugaban hukumar ta NEMA, Mustapha Habib Ahmed ya sake jaddada aniyar sabuwar gwamnatin Bola Ahmad Tinubu na magance kalubalen da matasa ke fuskanta.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...