An damke tsohon minista Adoke a Dubai

Adoke

Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa watau Interpol ta damke tsohon ministan shari’ar Najeriya bisa zargi sa da hannu a wata badakalar cin hanci kan danyen mai na fiye da dala biliyan daya.

Lauyan Mr Mohammed Bello Adoke ya tabbatar da tsare tsohon ministan a Dubai, amma ya ce bisa wani sammaci ne da lokacinsa ya wuce.

A baya Mr Adoke ya ce bai ci komai ba game da wata yarjejeniyar sayar da wata rijiyar mai a shekara ta 2011.

A cikin watan Afrilu ne hukumar yaki da rashawa a Najeriya – EFCC ta ba da sammacin kama shi tare da tsohon ministan man kasar, Dan Etete da kuma wani manaja a kamfanin mai na Italiya mai suna Eni.

Lamarin ya janyo shari’a mai tsawo tsakanin gwamnatin Najeriya da wasu kusoshi a kamfanonin mai na Eni da kuma Shell.

Sai dai duk kamfanonin biyu sun musanta aikata ba dai-dai ba.

More from this stream

Recomended