Jam’iyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan jam’iyar,Hajiya Maryam Sulaiman Mairusau bayan da ta soki gwamnan jihar,Mallam Uba Sani.
Dakatarwar da aka yiwa Mairusau na ɗauke ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 31 ga watan Maris da Ali Maishago shugaban matsabar Badarawa/Malali da kuma sakataren mazaɓar Zakka Bassahuwa suka sanyawa hannu.
Shugabannin mazaɓar sun ce an dakatar da ita ne kan kalaman da tayi na ɓata sunan gwamnan jihar.
A wata hirar da ta yi da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa, Mairusau ta caccaki gwamnan jihar biyo bayan kalaman da yayi na cewa tsohon gwamnan jihar,Mallam Nasiru El-Rufai ya bar masa ɗimbin bashi.
Sanarwar ta ce dakatarwar za ta cigaba har sai an kammala bincike.