An Dakatar Da Shugabar Matan Jam’iyar APC Ta Jihar Kaduna

Jam’iyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan jam’iyar,Hajiya Maryam Sulaiman Mairusau bayan da ta soki gwamnan jihar,Mallam Uba Sani.

Dakatarwar da aka yiwa Mairusau na ɗauke ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 31 ga watan Maris da Ali Maishago shugaban matsabar Badarawa/Malali da kuma sakataren mazaɓar Zakka Bassahuwa suka sanyawa hannu.

Shugabannin mazaÉ“ar sun ce an dakatar da ita ne  kan kalaman da tayi na É“ata sunan gwamnan jihar.

A wata hirar da ta yi da kafar yaÉ—a labarai ta DCL Hausa, Mairusau ta caccaki gwamnan jihar biyo bayan kalaman da yayi na cewa tsohon gwamnan jihar,Mallam Nasiru El-Rufai ya bar masa É—imbin bashi.

Sanarwar ta ce dakatarwar za ta  cigaba har sai an kammala bincike.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...