Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta bayar da sanarwar kawo karshen dokar hana fita ta tsawon sa’a 24, da aka sanya a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook.
A ranar Laraba ne dai rundunar ƴan sandan Kano ta sanya dokar bayan yanke hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna, da ya soke nasarar Abba Kabir Yusuf, tare da ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamna.