Connect with us

Hausa

An dage shari’ar Babachir Lawal

Published

on

Babachir a kotu

Image caption

Babachir a kotu

Wata kotu da ke zamanta a Abuja, birnin tarayyar Najeriya, ta dage shari’ar tsohon sakataren gwamnatin tarayya a kasar Babacir Lawal zuwa ranar Laraba.

Kotun dai ta bayar da umarnin cewa hukumar EFCC ta ci gaba da tsare Mista Lawal.

A lokacin sauraren karar, lauyan Mista Lawal ya bukaci da a bai wa wanda yake karewa beli.

Amma lauyoyin EFCC da suka shigar da karar Babachir suka nemi kotu ta yi watsi da bukatar bayar da belinsa.

EFCC na zargin tsohon sakataren gwamnatin ne da laifin karkatar da kudaden da aka ware wa ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Wannan zargin ne ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya kore shi daga gwamnatinsa.

Tun bayan sauke Babachir daga mukaminsa, ‘yan Najeriya ke ta ce-ce-ku-ce musamman kan tafiyar hawainiya da gwamnatin Buhari ke yi wajen gurfanar da Mista Lawal a gaban kotu.

Wannan shari’ar na zuwa ne kasa da mako daya a gudanar da babban zabe a kasar.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Abubuwan da suka faru a lik ɗin Firimiya

Published

on

Fermino da sauran 'yan wasan Liverpool na murnar bal din da ya ci

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallayen da Roberto Firmino da Sadio Mane suka ci su suka ba wa Liverpool maki uku

masu rike da kofin Zakaran Zakaru na Turai Liverpool sun ci gaba da samun nasara a kakar da aka shiga inda suka yi galaba a gidan Southampton, St Mary da ci 2-1 a wasan mako na biyu na Premier.

Sadio mane ne ya fara daga raga a wasan da kungiyar ta Jurgen Klopp ta yi nasara da ci 2-1, bayan da daman ya ciu biyu a karawar da Reds din suka doke Chelsea a fanareti a Istanbul ranar Laraba.

Roberto Firmino ya kara ta biyu, kafin kuma golan Liverpool din Adrian ya tafka kuskuren da ya ba wa Danny Ings damar zare daya bayan wasan ya yi nisa an kusa tashi.

Zakarun gasar ta Premier kuwa Manchester City a karon farko tun watan Disamba na 2018 sun barar da maki biyu a gida, bayan da suka yi canjaras 2-2 da Tottenham.

‘Yan City din sun ga samu sun ga rashi bayan da na’urar bidiyo mai taimaka wa alkalin wasa, ta nuna cewa bal din da Gabriel Jesus ya ci a daidai lokacin tashi daga wasan ba halartacciya ba ce.

Tun a kashin farko na wasan Raheem Sterling ya ci wa City bal din farko, amma nan da nan ba tare da bata wani lokaci ba Erik Lamela ya farke ta.

Sergio Aguero ya kara ci wa City ta biyu, kafin kuma Lucas Moura ya rama, bayan da ya yi canji ya shigo.

Teemu Pukki ya samu rana inda ya ci uku rigis, a wasan da bakin Premier, Zakarun gasar Championship na kakar da ta wuce Norwich City suka farfado daga kashin da suka sha na wasansu na farko a hannun Liverpool, suka casa Newcastle United 3-1.

Dan wasan gaban na Finland wanda yanzu ya ci bal hudu a wasa biyu na Premier, ya fara daga raga ne tun a kashin farko na wasan, kafin kuma ya kara biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Jonjo Shelvey ya ci wa kungiyar ta kociya Steve Bruce, Newcastle United, ladan gabe daya.

Aston Villa kuwa za ta ci gaba da jiran lokacin da za ta yi nasararta ta farko ta kakar nan, bayan da ta yi rashin nasara a gidanta da ci 2-1, a hannun Bournemouth.

Fanaretin da Joshua King ya ci a minti biyu na wasan, da kuma kwallon farko da dan wasan Liverpool da ya tafi aro Harry Wilson ya ci ta ba wa bakin na kociya Eddie Howe damar kankane wasan tun da farin-farko.

Sai dai Douglas Luiz ya motsa masu masaukin bakin da bal daya da ya farke musu a kashi na biyu na wasan.

Dan wasan na Brighton ta saya da bazara Leandro Trossard ya farke kwallon da Javier Hernandez ya fara daga raga da ita, a wasan da aka tashi 1-1 da West ham a filin wasa na Amex Stadium.

Tun da farko na’urar bidiyo mai taimaka wa alkalin wasa ta nuna cewa bal din da Trossard ya fara ci a kashin farko na wasan , ya yi satar gida, amma kuma ya samu damar farkewa wadda Hammers din suka fara ci a minti na 61.

Ita kuwa Everton kwallon da Bernad ya ci a minti na goma da wasa, ita kadai take bukata ta yi nasara a gida tsakaninta da tsohuwar kungiyar kociya Marco Silva, Watford.

A ranar ta Asabar, tun da farko a karawar da aka yi a filin Emirates bal din da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci ta ba wa Arsenal damar galaba a kan Burnley da ci 2-1.

Tun da farko Gunners din ke kan gaba bayan da Alexandre Lacazette ya ci mata bal dinsa ta farko bayan ya dawo daga jinya, amma kuma Ashley Barnes ya farke wa bakin kafin tafiya hutun rabin lokaci.

A ranar Lahadi kuwa wasanni biyu ne za a yi a gasar ta Premier, inda sabbin zuwa Sheffield United za su karbi bakuncin Crystal Palace a wasansu na farko na gida da karfe 2:00 na rana agogon Najeriya.

Ita kuwa kungiyar kociya Frank Lampard, Chelsea za ta nemi kauce wa rashin nasara a karo na uku a jere a cikin kwana takwas a wasan da za ta karbi bakuncin Leicester City a Stamford Bridge da karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Rubewar hakori: kun san yanda zaki ke kassara lafiyar hakoran yara?

Published

on

Rashin kula na daga cikin abubuwan da suka sa yara a Afirka suka fi fama da ciwon hakori

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Likitocin hakori a Birtaniya sun bukaci gwamnatin kasar da ta sa makarantun kasar su daina bai wa yara cimaka mai zaki domin maganace rubewar hakora.

Sun ce hakan na da alfanu domin shawo kan matsalar wadda ke addabar kimanin kashi daya cikin hudu na yara ‘yan shekara biyar.

Haka nan masanan a harkar lafiya na bukatar ganin an kara sanya ido kan yadda yara ke wanke baki.

Kafin sauka daga mukami, Firaminista Theresa May ta sanar da wasu shirye-shirye na bunkasa lafiyar hakoran yara.

Sai dai sashin lafiyar hakori na kasar ya ce duk da an samu ci gaba a fannin, akwai bukatar a kara azama.

Wani kwararren likita a Najeriya Dakta Tanko Zakari, na asibitin koyarwa na Aminu Kano ya ce yara a yankin nahiyar Afirka sun fi na yankin Turai fama da wannan matsala ta rubewar hakori.

Ya ce, yawancin abubuwan da ke haddasa wannan matsala shi ne rashin ilimi da kuma hangen nesa game da lafiyar yara.

Sai dai ya ce matakin rage shan zaki, da kuma rungumar dabi’ar wanke baki za su iya hana rubewar hakora.

A cewarsa ‘ya kamata iyaye su tabbatar yara na wanke baki a kowane lokaci, a lokacin da za su tafi makaranta, da kuma lokacin da za su kwanta bacci.’

Shi dai bangaren kula da lafiyar hakorin na Birtaniya ya fitar da wani rahoto, inda ya bayar da shawarar daukan wasu matakai domin shawo kan matsalar rubewar hakori ga yara.

Shawarwarin sun hada da:

  • Dukkanin makarantu su fito da tsarin lura da yadda yara ke goge hakori.
  • Dukkanin makarantu su daina bai wa yara abinci mai sukari kafin shekarar 2022.
  • A takaita tallace-tallacen abinci masu dauke da sukari sosai.
  • A rage sukari da ake sanyawa cikin abincin jarirai da kamfanoni ke hadawa.
Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Mutane 5 aka halaka a rikicin Benue – ‘yan sanda

Published

on

Yan sanda a jihar Benue sun tabbatar da kashe mutane 9 a wasu garuruwa dake karamar hukumar Katsina Ala ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Catherine Anene ta ce rikicin da ya faru a Katsina Ala rikici ne wanda yake yawan faruwa a tsakanin kabilun Ikurav da Shitile .

“Rikicin ya faru a kauyuka uku. Babu dalilin kai harin saboda.An gudanar da ganawa a lokuta da dama tsakanin kabilun amma aka kasa cimma matsaya,”

Rahotanni sun bayyana cewa mayaka daga bangarorin kabilun biyu; Shitile da Ikurav sun kai ma juna hari da safiyar ranar Asabar har ta kai ga an samu asarar rayuka.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: