Shugaban Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, Hon. Nasara Rabo, ya bai wa wani jami’in ‘yan sanda, Difi’o Idris Ibrahim, zunzurutun kudi har naira miliyan 1, bisa ƙin amincewa da wasu maƙudan kudade da wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ya bayar domin kar a bincike shi.
Rabo wanda ya bayyana hakan a cikin wata takardar shawarwarin da ya fitar a ranar Litinin din da ta gabata ya bayyana cewa DPO din ya kama wani mai garkuwa da mutane a ranar 22 ga watan Janairun 2024, wanda ya yi yunkurin ba shi cin hanci da makudan kudade domin a datse binciken ko kuma a murguda aikin binciken.
Amma ɗan sandan ya ki amincewa da cin hancin kuma ya sha alwashin ba da damar doka ta yi aiki yadda ya kamata saboda kishin ƙasa da kuma tsayin daka wajen tabbatar da adalci.
“Wannan kokari na musamman da kuka yi ba iya alfahari rundunar ‘yan sandan Najeriya suka yi ba, har ma ya sanya mutanen karamar hukumar Kagarko, na jihar Kaduna, da Najeriya baki daya, ya kara da cewa wannan shaida ce da ta dace.