Amurka Na Razana Duniya Game Da Cutar Coronavirus – AREWA News

L

Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya caccaki Amurka a game da yadda ta ke hadassa fargaba a duniya kan cutar Coronavirus.

Shugaba Rohani, ya ce Amurka na razana duniya game da batun cutar data bulla a kasar, sannan ta ke ci gaba da yaduwa a wasu kasashen duniya.

‘’ Bai kamata mu kyale Amurka ta hadassa mana wani sabon virus ba, wanda shi ne matsanancin tsoro’’ inji shugaba Rohani.

Rohani, ya kara da cewa, Amurka da kanta tana fama da cutar ta corona, sannan mutane 16,000 suka mutu a can din sakamakon mura, amma bata magana akan batun.

Kalamman na shugaba Rohani, na zuwa ne kwana guda bayan furucin sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, na cewa Iran na boye gaskia akan abunda ya shafi cutar mai shafar numfashi ta Covid-19.

Kawo yanzu dai mutane 19 aka tabbatar da sun mutu sanadin cutar a Iran, sai kuma wasu 139 da suke jinyarta.

Iran dai ta sha alwashin daukar duk matakan da suka dace na murkushe cutar.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...