Amurka Na Ci Gaba Da Tallafawa Najeriya Don Kyautata Rayukan Al’umma – AREWA News

Jakadar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard, ta dukufa ga ziyarar jihohin Najeriya wadanda kasar take hulda da su domin ci gaba da tallafa musu.

An kwashe shekaru masu yawa kasar Amurka ke kawance tare da bayar da tallafi ga Najeriya da ma wasu kasashen duniya domin kyautata rayukan jama’a tare da samar da ci gaba mai dorewa.

A Najeriya, kasar Amurka tana bayar da tallafi a sassa daban daban kama daga sashen kula da kiyon lafiya da ilimi da Noma da makamashi da sauransu, kuma ta kashe makudan kudade a wadannan sassan.

A jihar Sokoto kadai, Amurka ta bada tallafin dala miliyan 122 a fannin kiyon lafiya daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Akan haka ne wakilin Sashen Hausa Muhammad Nasir ya ziyarci wani asibiti da ke samun tallafi daga shirin bunkasa kiyon lafiya na hukumar raya kasashe masu tasowa ta kasar Amurka (USAID) Kuma ya samu ma’aikata bakin aiki.

Domin tabbatar da ayyukan da ke gudana a karkashin kawancen Amurka da Najeriya yadda ya kamata yasa jakadar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, ta dukufa ga ziyarar jihohin Najeriya da zummar karfafa huldar da ke Tsakani, duk kuwa da fama da annobar coronavirus da ake yi.

Amurka dai tana nuna gamsuwa kan yadda gwamnatocin da take hulda da su ke bayar da hadin kai wajen amfanar da al’ummomin su.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...