Amurka da Birtaniya sun soki kasashen Sahel kan rikicin yankin | BBC Hausa

Shugabanin kasashen kungiyar G-5 Sahel a taron Bamako na kasar Mali

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugabanin kasashen kungiyar G-5 Sahel a taron Bamako na kasar Mali

Birtaniya da Amurka sun gaya wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa gwamnatocin kasashen Sahel da ke Afirka ta Yamma ba sa yin abin da ya kamata domin kawo karshen tashin hankalin da ke addabar yankin.

Duk da kasancewar dubban dakarun yankin da na wasu kasashe a Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, ana samun karuwar hare-haren kungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke da alaka da Al Qaeda da kuma IS.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akwai sojojin Faransa 4500 a yankin na Sahel

Bisa ga dukkan alamu baki kusan ya zo daya cewa abubuwan da ke haddasa ko kuma suka haddasa hare-hare da tashin hankalin masu tayar da kayar baya da ke da nasaba da addini a yankin na Sahel, a kwai rashin jituwa da zaman doya da manja tsakanin saboda filayen kiwo ko noma da ruwa, wanda akwai bukatar show kan wannan matsala.

Hakkin mallakar hoto
MSF

Da yake jawabi ga ‘yan kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya, mataimakin jakadan Amurka a Majalisar, ya ce matakin soji kadai da ake dauka a yankin ba zai raba alumma da tashe-tashen hankali ba.

Ya ce akwai bukatar samun yanayi na juriya da hakurin zama tare da samun gwamnatoci na gari da kuma wanzuwar kungiyoyin kare hakkin jama’a masu karsashi, kafin a samu zaman lafiya da ci gaba a yankin.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Shi ma jakadan Birtaniya a Majalisar ta Dinkin Duniya ya kara ne da cewa, dole ne a magance matsalar cin hanci da rashawa da rashin ayyuka da karancin ababan bunkasa rayuwar jama’a da kawar da matsalar rashin dama ga matasa, kafin yankin na Sahel ya fito daga kangin tashin hankali na masu tayar da kayar-baya da koma-baya da yake ciki.

Sai dai kuma duk da wannan a yanzu shugabannin kasashen yankin na neman karin taimako na soji, ganin yadda daruruwan sojojinsu ke fadi-tashin rike iko a inda suke gwagwarmaya da masu tayar da kayar baya.

Ana sa ran a watan Janairu Faransa da ke da dakaru 4500 a fadin yankin na Sahel za ta yi taron koli na tsaro domin tattauna batun kasancewar sojin nata a yankin.

An ruwaito hafsan hafsoshin Faransar Janar Francois Locontre, yana bayyana cewa makomar yankin na Sahel za ta danganta ne da abin da zai faru a shekara mai zuwa.

Ya bayyana cewa idan aka bari rikicin da ake fama da shi a yanzu ya dabaibaye yankin, ‘yan kungiyar IS za su mamaye shi.

Ya bayyana cewa matakan da sojoji ke dauka kadai ba za su karya ‘yan kungiyar ba, da kuma kawo karshen wasu rikice-rikice a yankin na Sahel, sai an kawo wata mafita ta hanyar siyasa.

Janar Francois ya kare dakarun Faransar da ke yakar masu ikirarin jihadi a yankin na Sahel. inda ya ce Faransa za ta kai wannan yaki mataki na gaba.

More News

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da suka yi bacci a lokacin da suke tsare da mutanen da suka sace

Jami'an Æ´an sanda sun samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane bayan da suka buge da sharar bacci a lokacin da suke tsare...