Aminu Daurawa: Abin da ya sa muka bar gwamnatin Ganduje

Shaikh Aminu Daurawa

Wasu manyan malaman addinin musulunci a Kano da suka hada da Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Shaikh Abba Adam Koki, shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano da Dr Muhammad Nazifi Inuwa da kuma Malam Abubakar Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje.

Wata sanarwa da malaman suka sanya wa hannun ta bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda ayyukan da suke gabansu.

Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da shi ta waya, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun fita daga gwannatin ne saboda sun ga ba a bukatar aikinsu.

Shi kuwa a cikin takardar da ya mika ta murabus dinsa Shaikh Abba Adam Koki ya ce ya ajiye aikin ne saboda dalilan rashin lafiya.

Shaikh Daurawa dai shi ne babban kwamandan Hisbah ta jihar Kano, shi kuma Shaikh Abba Koki shi ne shugaban hukumar alhazai ta jihar.

Malam Nazifi Inuwa ya rike mukamin kwamishina na biyu a hukumar Zakka ta jihar Kano, yayin da shi kuma Malam Abubakar Kandahar ya rike mukamin kwamishinan shari’a na daya na jihar ta Kano.

Dangantaka tsakanin gwamnan na Ganduje da wasu daga cikin malaman ta jima da yin da tsami, inda ake zaune ta ciki-na-ciki.

Murabus din malaman na zuwa ne kasa da mako daya bayan gwmanan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai wasu bara-gurbi a hukumar Hisbah.

Yayin da yake jawabi a wajen taron auren zawarawa da aka gudanar a makon farko na wajen Mayu, gwamnan ya ce ana muna-muna da cuwa-cuwa a hukumar Hisbah, abin da ya ce dole ne a tsaftace hukumar.

Dangantakar ta kara yin tsami ana daf da zaben gwamna, bayan da wani bidiyo da aka watsa ta kafofin sada zumunta ya nuna wasu malaman da ke rike da mukamin gwamnati sun kai ziyarar goyon baya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar PDP.

Kwankwaso shi ne babban abokin hamayyar gwamna Ganduje, duk da cewa ba shi ya nemi takarar gwamnan ba.

Mafi yawan malaman da suka ajiye aikin dai tsohon gwamna Kwankwaso ne ya nada su a mukaman, yayin da shi kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da aiki da su bayan ya zama gwamna a 2015.

More News

Tinubu ya bada umarnin sakin yaran da aka gurfanar a gaban kotu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin  gaggauta sakin yaran nan da aka gurfanar a gaban kotu inda ake tuhumarsu da zargin...

Sojoji sun kama ɗan fashin daji Habu Dogo

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce sojojin  ta ce dakarun soja a makon da ya wuce sun samu  nasarar kama gawurtaccen ɗan fashin daji, Abubakar...

Mutane biyu sun mutu a rikici tsakanin sojoji da ƴan sanda a jihar Nasarawa

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ce mutane biyu aka tabbatar da sun mutu bayan wani faɗa da aka yi tsakanin sojoji da ƴan...

Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci ranar Litinin

Shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci a ranar Litinin bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da su. Mashawarci na musamman ga shugaban...