Ambaliya ta yi barna a Zamfara

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da dama a Gusau babban birnin jihar Zamfara, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a yammacin Lahadi.

An rawaito cewa ruwan sama da aka kwashe sama da awa daya ya tafka barna a yankuna da dama na babban birnin jihar inda aka ga mazauna garin suna kwashe dukiyoyinsu daga gidajensu.

Hanyoyi da dama, musamman a unguwar Gengeri Megamu sun cika da ruwa, wanda hakan ya sa masu ababen hawa ba su iya wucewa.

A cewar wani mazaunin garin, Alhaji Malami, abin ya yi muni, inda ya kara da cewa mutane da dama sun yi asarar dukiyoyinsu sakamakon ruwan sama mai yawa.

“Gwamnatin jihar ta san cewa an dade ana samun irin wannan lamari tsawon shekaru amma ba a dauki matakin magance matsalar ambaliyar ruwa a yankin ba.

“Yawancin yankunan ruwa ne kuma babu rijiyoyin da aka gina don su rage ambaliyar,” in ji shi.

More from this stream

Recomended