Allah Ya yiwa Daraktan Fim din ‘Izzar So’ rasuwa

Allah ya yiwa Nura Mustaphae Waye rasuwa a safiyar yau.

Kafin rasuwarsa Mustapha ya kasance mai bayar da umarnin shirin wasan Hausa mai dogon zango na Izzar So.

Lawan Ahmad, mashiryin shirin fim din Izzar So shi ne ya sanar da labarin mutuwar ta sa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Fim din na Izzar So ya samu karbuwa da dama a wurin mutane masu dimbin yawa saboda fadakarwar da yake dauke da ita.

More from this stream

Recomended