Bill Gates, wanda ya kafa Microsoft, da Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote, sun gana da shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Dayo Olusegun, mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yada labarai ne ya wallafa a shafinsa na Twitter game da taron.
A cewar Olusegun: “Mr @BillGates, shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates kuma wanda ya kafa Microsoft ya isa fadar shugaban kasa a Villa tare da Alhaji @ Aliko Dangote domin ganin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR).”
Ku tuna cewa Dangote ya bayyana a makon jiya cewa Tinubu da Gates za su yi taro a yau.