Aisha Buhari ta caccaki mai magana da yawun Buhari | BBC Hausa

Aisha Buhari

Mai dakin shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta wallafa wani rubutu da yake ta karakaina a shafukan sada zumunta, inda da kanta ta caccaki mai magana da yawun Buhari, malam Garba Shehu.

Rubutun da aka wallafa mai taken “Garba Shehu na wuce gona da iri”, mai dakin shugaba Buharin ta nuna yadda mai magana da yawun mijin nata ke ‘yi wa iyalan shugaban zagon kasa’.

Aisha Buhari ta ce “Garba Shehu na daya daga cikin masu kware wa Buhari baya kasancewar yaron abokin hamayyar Buharin ne a zaben shugaban kasa, Alhaji Abubakar.”

Ta kuma yi zargin Garba Shehu da yin sama da fadi da wasu kudaden ‘yan jaridu a fadar shugaban kasa.

Har wa yau, Aisha Buhari ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda Garba Shehu yaki cewa uffan a lokacin da ake yada jita-jitan auren Buhari da minista Sadiya Farouk.

Aisha Buhari ta kuma zargi Garba Shehu da hannu wajen dakatar da dan jaridar gidan Talbijin na NTA, Aliyu Kabir da ma’aikatar ta yi masa kan wata hira da aka yi zargin shi ya yi wa matar shugaban kasar.

To sai dai da BBC ta tuntubi Malam Garba Shehu kan batun, ya ce ba zai sa-in-sa da mai dakin mutumin da yake yi wa aiki ba.

More News

An kwaso ƴan Najeriya 180 daga ƙasar Libiya

Ofishin hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA a jihar Lagos ya ce sun karɓi ƴan Najeriya 180 da aka dawo da su gida...

Yawan mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwalen jihar Niger ya kai 42

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Niger NSEMA ta ce yawan mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale da ya faru a jihar sun...

Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da...

Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka...