Aisha Buhari Ta Bude Wata Cibiyar Kula Da Mata Masu Juna Biyu A Yola

Ya yin da Najeriya ke shirin bikin ranar dimokaradiyya ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2019, Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari,ta jagoranci wasu matan shugabanin Afrika zuwa Yola jihar Adamawa, domin bude wata cibiyar kula da mata masu juna biyu da kuma kaddamar da wani sabon shiri na rage talauci ga al’ummar karkara, karkashin hukumar samar da aikin yi ta NDE.

A cikin jawabin ta Aisha Buhari, ta ce “A madadin sauran matan shugabanin Afrika biyar da suka zo don taya Najeriya da yan Najeriya murnar ranar dimokaradiyya, uwar gidan shugaban kasar Ghana Madam Rabecca Akufo Addo,ta ce matan shugabanin kasashen Afrika kan taka rawa ta fannonin ci gaba duk da cewa basu da wani kasafin kudi da akan basu.

Ta kuma yabawa Aisha Buhari, bisa wasu ayyuka da ta kirkiro na ci gaban al’umma. Ita ma a jawabinta, uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta ce gidauniyarta ta ‘Future Assured’ za ta ci gaba da hada kai da sauran cibiyoyi don tallafawa al’umma musamman masu karamin karfi.

Dakta Nasir Ladan, dake zama shugaban hukumar ta NDE a Najeriya, ya bayyana manufar wannan shiri da aka kaddamar a Yola.

Victoria Ajiya, daya daga cikin matan da zasu ci gajiyar wannan shirin ta bayyana farin cikinta inda ta ce “Ina farin ciki da Allah ya yi amfani da uwar mu, wajen samun wannan dama na koyon sana’a don dogaro da kai.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...