Afirka ta sa Faransa da Italiya cacar baki

Luigi di Maio

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Kasar Faransa ta kira jekadiyar Italiya bayan mataimakin Firaministan Italiya, Luigi di Maio, ya yi zargin cewa na Faransa ci da gumin Afirka tare da kara rura kwararar ‘yan ci-rani.

A ranar Lahadi ne, Luigi di Maio ya yi kira ga Tarayyar Turai ta kakaba takunkumi ga Faransa saboda manufofinta a Afirka.

Ya ce, “har yanzu Faransa ba ta daina mullkin mallaka ba kan kasashen Afirka guda 10.”

“Kasashen turai ne suka sa mutane yin kaura, musamman Faransa da har yanzu ba ta daina yi wa kasashen Afirka mulkin mallaka ba,” in ji shi.

Ya kuma ce ba don Afirka ba, da yanzu Faransa tana matsayi na 15 a jerin kasashe masu karfin tattalin arziki maimakon na shida a duniya.

Ya kuma zargi tattalin arzikin Faransa da ci da gumin wasu kasashen Afirka ta hanyar amfani da kudinta na CFA.

Wannan ne ya sa ofishin harakokin wajen Faransa ya kira jekadiyar Italiya Teresa Castald a Paris domin ya ji kokenta da kuma yin karin bayani.

Gwamnatin Italiya ta yanzu dai ta sha yin cacar-baki da Faransa kan ‘yan ci-rani da zanga-zanga da kuma al’adu.

Me suke jayayya akai?

Dangantaka tsakanin Faransa da Italiya ta kara tsami ne tun kafa sabuwar gwamnatin Italiya a 2018.

Danganta tsakanin kasashen biyu ta fi tsami ne kan batun ‘yan ci-rani. Kasashen biyu na jayayya ne kan yadda Faransa ke taso keyar ‘yan ci-rani zuwa kan iyakar Italiya.

Italiya ta zargi Faransa da kin karbar ‘yan ci-rani, bayan Faransa ta ce Italiya ba ta taimaka wa masu aikin ceto ‘yan ci-ranin a teku.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Sama da ‘yan ci-rani 4,200 aka ruwaito sun tsallaka zuwa Turai a cikin kwanaki 16 na farkon shekarar 2019
.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...