Adadin wadanda suka mutu a harin Boko Haram ya kai 65

VOA Hausa

Shugaban karamar hukumar Bulama, Muhammed Bulama, ya tabbatar da mutane 65 suka mutu kana wasu goma kuma suka jikata, kana ya ce yana gani wannan harin martani ne da Boko Haram ta kai bayan ‘yan kauyen sun kashe mayakanta 11 a makon da ya gabata.

A makon da ya gabata ne ‘yan Najeriya suka cika shekaru goma da fuskantar hare haren Boko Haram da suka hallaka sama da mutane dubu talatin suka fidda miliyoyin mutane a cikin gidajensu kana suka haddasa matsalar bukatar taimako a duniya. Kungiyar ta ‘yan tsaurin ra’ayin Islama tayi fice wurin yin garkuwa ‘yan mata ‘yan makaranta da kuma sakawa matasa maza da mata bama bamai a jikinsu suna kai hare hare a kasuwanni da wuraren ibada da ma wurare masu cunkoson jama’a.

Kungiyar ‘yan ta’addan da take yada tsauraran ra’ayin Islama da kuma kalubalantar ilimin nasara, ta musunta ikirarin da gwamnatin Muhammadu Buhari tayi cewa ta murkusheta. Rikicin Boko Haram dai ya shiga harkasashe masu makwabtaka da Najeriya da suka hada Nijer, Chadi da kuma Kamaru.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...