AC Milan ta kafa tarihin cin kwallo a kankanin lokaci a Serie A

AC Milan

Bayanan hoto,
Rafael Leao ya ci kwallo na uku kenan a gasar Serie A ta bana

Ranar Lahadi AC Milan ta yi nasarar doke Sassoulo da ci 2-1 a wasan mako na 13 a gasar Serie A da suka fafata.

Milan ta fara cin kwallo ce ta hannun Rafael Leao, kuma ita ce wadda aka zura a kankannin lokaci a tarihin gasar Serie A ta Italiya.

Dan wasan tawagar Portugal, mai shekara 21, ya zura kwallo a ragar Sassaoulo ne a dakika shida da fara tamaula.

Kwallon da Leon ya ci a ranar Lahadi ya kawo karshen tarihin da Paolo Poggi ya kafa a wasan da ya ci Fiorentina a dakika 8.9 ranar 2 ga watan Disambar 2001.

Dan wasan tawagar Belgium, Alexis Saelemaekers ne ya ci wa Milan na biyu, inda Domenico Berardi ya zare kwallo daya daga cikin wadanda aka ci Sassuolo.

Da wannan sakamakon Milan ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Inter Milan wadda ta doke Spezia 2-1.

Kwallon da Leao ya zura a raga ranar Lahadi tana kan gaba a Premier League da Shane Long na Southampton ya ci Watford a dakika 7.69 ranar 23 ga watan Afirilun 2019.

More News

Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban RiÆ™on Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam'iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam'iyar. Mai Shari'a  Peter Lifu shi...

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...