Abubuwan da suka faru a duniyar wasanni daga Janairu zuwa Disamban 2020

Premier League

Shekara ta 2020 ta zama mai Æ™alubale a fadin duniya har da bangaren wasanni, bayan da cutar korona ta dagula al’amura a fadin duniya.

Cutar ta sa a É—auke wasu wasanni, an koma buga wasu ba magoya baya, bayan da wasu kungiyoyin suka bukaci ‘yan wasa su rage albashi, wasu ma suka yafe na wasu watanni.

Cikin shekarar nan fitattun Æ´an wasa sun mutu da suka hada da Diego Maradona da Kobe Bryant da sauransu.

Duk da bullar cutar korana an ci gaba da wasanni, bayan da aka dauki matakan hana yada annobar, hakan ya sa an samu yan wasa da kungiyoyi da jami’ain da suka taka rawar gani a shekarar 2020.

Watan Janairu

Dan kwallon tawagar Italiya, Daniele De Rossi ya yi ritaya daga taka leda. De Rossi, ya buga wa Roma tamaula kaka 18.

A karon farko Dan kwallon tawagar Senegal da Liverpool, Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2019.

Tsohon zakaran ƙwallon kwandon Amurka da Los Angeles Lakers, Kobe Bryant da yarsa Gianna suka mutu a hatsarin jirgi a California.

Bryant ya lashe kofin NBA a Lakers karo biyar 2000 da 2001 da 2002 da 2009 da kuma 2010).

Hukumar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya ta soke gasar da ya kamata China ta karbi bakunci a Maris din 2020. An kuma cimma wannan matsayar saboda bullar cutar korona.

Watan Fabrairu

‘Yar kasar Amurka, Sofia Kenan ta lashe gasar kwallon tennis ta Australin Open.

A bangaren maza kuwa, Novak Djokovic ne ya zama zakara a gasar ta Australian Open ta 2020.

Dan damben Burtaniya Tyson Fury ya kawo karshen shekara biyar da Deontay Wilder ya yi da kambun WBC.

Watan Maris

Aka tsare fitatcen dan kwallon Brazil, Ronaldinho da dan uwansa Roberto Assis a Paraguay kan samunsu da laifin shiga kasar da fasfo na jabu.

Hukumar kwallon kwandon Amurka ta dakatar da wasannin NBA, bayan da dan wasan Utah Jazz, Rudy Gobert ya kamu da cutar korona.

Aka dakatar da wasannin UEFA Champions League da na Europa League don gudun yada cutar korona.

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta dage Euro 2020 zuwa shekara daya saboda cutar korona.

Haka ma aka dage Copa America na 2020 zuwa shekara daya don gudun yada annobar.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta dage Fifa Club World Cup da ya kamata a yi a China.

UEFA ta dage wasannin karshe na Champions League da na Europa League saboda gudun yada annobar.

Kamitin Olympic na duniya y adage wasannin da birnin Tokyo zai karbi bakunci, sakamakon bullar cutar korona.

Kwamitin Olympic na duniya ya ce zai gudanar da wasannin tsakanin 23 ga watan Yuli zuwa 8 ga watan Agusta a Tokyo da na nakasassu tsakanin 24 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumbar 2021.

Watan Afrilu

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta soke duk wani wasa tsakanin kasa da kasa don gudun yada cutar korona.

Aka dage gasar tseren motocin Formula 1 da ya kamata a yi a Canada, saboda tsoron yada cutar korona.

Aka dage gasar tseren kekuna ta Tour de France zuwa 29 ga watan Agusta, saboda cutar korona.

Aka daga gasar Berlin Marathon a karon farko, wadda aka fara tun 1974.

UEFA ta dage wasannin kwallon mata UEFA Euro 2021 zuwa 2022, saboda cutar korona.

Fifa ta sanar da za ta raba kudi dalar Amurka 150 ga mambobinta don rage radadin cutar korona.

Aka soke gasar kwallon Faransa aka bai wa Paris St Germain kofi a matsayin wadda ta lashe kakar 2020.

Watan Mayu

Aka amince hukumomin kwallon kafa su fara amfani da dokar sauya yan wasa biyar a cikin fili, saboda cutar korona.

An ci gaba da wasannin Bundesliga a Jamus, bayan dakatar da fafatawar cikin watan Maris.

Gasar Premier League ta Ingila ta ce za ta ci gaba daga 17 ga watan Yuni ba tare da ‘yan kallo ba.

Serie A kuwa ta tabbatar cewar 20 ga watan Yuni za a ci gaba da fafatawa ba ‘yan kallo.

Mahukuntan gasar Spanish La Liga suka sanar da za a ci gaba da wasanni ranar 11 ga watan Yuni.

Watan Yuni

Napoli ta lashe Copa Italia, bayan doke Juventus 4-2 a bugun fenariti.

New York Marathon da ya kamata a yi a Nuwamba aka dage zuwa Nuwambar 2021 don gudun yada cutar korona.

Fifa ta sanar cewar Australia da New Zealand ne za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a kwallon mata a 2023.

Liverpool ta lashe gasar Premier League a karon farko tun bayan shekara 30.

Barcelona ta dauki dan kwalon Juventus, Miralem Pjanic kan dalar amurka miliyan 67.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta dage gasar kofin Afirka na 2021 da ya kamata Kamaru ta karbi bakunci ta ce sai a 2022 za a buga saboda gudun yada cutar korona.

Watan Yuli

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi ya ci kwallo na 700 a raga a tarihin buga tamaularsa.

Bayern Munich ta lashe German Cup, bayan da ta doke Bayer Leverkusen 4-2.

Aka fara kakar Formula da Australian Grand Prix ta shekarar wadda aka dunga sauya lokuta, kuma direban Marsandi, Valtteri Bottas shi ne ya zama zakara.

UEFA ta sanar da dage dokar hana Manchester City shiga gasar Champions League shekara biyu.

Real Madrid ta lashe La Liga kuma na 34 jumulla, bayan doke Villareal 2-1.

Tsohon dan kwallon tawagar Jamus, Andre Schurrle ya sanar da yin ritaya daga taka leda.

Ba wanda aka bai wa kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2020 wato Ballon d’Or, saboda cutar korona.

Paris Saint-Germain ya lashe 2020 French Cup, bayan da ta doke Saint-Etienne 1-0.

Dan wasan tawagar Ingila da Leicester City, Jamie Vardy, ya zama mai yawan shekaru da ya ci kwallo a gasar cin kofin Premier League.

Watan Agusta

Arsenal ta lashe FA Cup na 14 jumulla, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea 2-1 a Wembley.

Ciro Immobile ya lashe takalmin zinare, bayan da ya ci kwallo 35 a wasa 36, shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Italiya da kuma nahiyar Turai.

Dan kwallon Manchester City, Kevin De Bruyne ya lashe kyautar dan kwalon gasar Premier League da ba kamarsa.

Sevilla ta lashe 2020 UEFA Europa League, bayan da ta doke Inter Milan da ci 3-2.

Bayern Munich ta lashe Champions League, bayan da ta doke Paris Saint-Germain 1-0.

Arsenal ta zama zakara a 2020 English FA Community Shield, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool da ci 5-4 a bugun fenariti

Zlatan Ibrahimovic ya sanar da zai koma AC Milan da taka leda.

Watan Satumba

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi ya sanar zai karasa kaka daya da ta rage masa a Barcelona.

Dominic Thiem ya lashe 2020 US Open, bayan doke Alexander Zverev.

Dan kwallon tawagar Wales, Gareth Bale ya koma Tottenham don ci gaba da buga gasar Premier League daga Real Madrid a matakin aro.

Atletico Madrid ta sanar da daukar Luis Suarez daga Barcelona.

Watan Oktoba

Bayern Munich ta lashe 2020 German Super Cup, bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 3-2.

Dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar Turai na 2020.

Manchester United ta sana da daukar dan kwallon Uruguayan, Edinson Cavani kan yarjejeniyar shekara a matakin wanda bai da kungiya.

Iga Swiatek bta doke Sofia Kenin ta kuma lashe 2020 French Open.

A karawar maza kuwa Rafael Nadal ne ya zama gwani, bayan da ya casa Novak Djokovic.

Los Angeles Lakers ta doke Miami Heat 106-93 ta kuma lashe kofin NBA a karon a shekara 10 kuma na 17 jumulla,

Dan kwallon Argentina, Pablo Zabaleta ya sanar da yin ritaya daga buga tamaula.

Watan Nuwamba

Bayanan hoto,
Gawar Maradona

Arsenal ta doke Manchester United 1-0 a gasar Premier League a Old Trafford a karon farko tun bayan 2006.

Direban Marsandi, Lewis Hamilton ya lashe 2020 Formula 1 ta duniya kuma kofi na takwas jumulla.

Tsohon dan wasan Barcelona da Argentina, Javier Mascherano, ya sanar da yin ritaya.

Fifa ta dage 2020 FIFA Club World Cup zuwa Fabrairun 2021, don gudun yada cutar korona.

Diego Maradona ya mutu tsohon dan kwallon Argentina da Napoli da Barcelona..

Tsohon dan kwallon tawagar Senegal, Papa Bouba Diop ya mutu.

Watan Disamba

Napoli ta sanar da sa sunan filinta zuwa Diego Armando Maradona.

Tsohon kocin Liverpool, Gerard Houllier ya mutu.

Robert Lewandowski ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa na 2020.

Dogon Kyallu ya zama sarkin damben gargajiya, bayan da ya buge Ali Kanin Bello a Kano.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...