Abinci da ya kamata ku ci idan kun haura shekara 40 a duniya

kayan lambu

Asalin hoton, Getty Images

Abinci wani sinadari ne da ke da matukar amfani ga bil adama wanda rayuwa ba za ta yiwuwa ba idan ba ka cin abinci musamman mai gina jiki.

Sai dai duk da muhimmanci abinci ga jikin bil adama ƙwararru na yawaita jan hankali kan alfanun ilimin sarrafa abinci da ya dace ake ci, da adadin da ya kamata mutum ya ci saboda lafiyarsa.

Haka zalika masana na yawaita gargadi da jan hankali kan irin abinci da ya kamata mutane suke ci bisa ga yanayin jiki da lafiyarsu da kuma batun shekaru.

Kamar lokacin da mutum ke tasowa akwai nau’ukan abinci da ake shawarta ya rinka yawaita ci, idan kuma shekaru sun ja ana bayar da shawawari irin abinci da ya kamata mutum yake ci don kara masa lafiya da garkuwar jiki.

Sauya cimaka a shekaru 40

A tattaunawarta da BBC, wata Æ™wararriyar likita da ke aiki da asibitin koyarwa ta jami’ar Ilorin da ke Najeriya, ta ce galibi daga shekaru 40 ake son mutum ya sauya salon abincinsa.

A cewar Dr Sadiya Musa yana da muhimmanci ga wanda shekarunsa suka kai 40 ya kula da lafiyarsa matuka saboda lokacin da shekarun mutum ke ƙaruwa ƙarfin jikinsa na raguwa.

Sannan lokacin ne cututtuka suka fi kama mutum ko bayyana a jikin mutum.

A dalilin haka ne masu wadannan shekaru suka fi bukatar cin abinci mai lafiya da zai ƙara musu karfi da kuma lafiya, in ji Dr Sadiya.

To kuma ce rashin lura da abincin da ake ci a waÉ—annan shekaru barazana ne ga lafiyar a yayin da cututtuka kamar hawan jini da ciwon suga da ciwon kafa ka iya kama mutum.

Dr Sadiya ta ce abincin da ya kamata mutum ya rinka ci da zarar ya cika shekaru 40 sun haÉ—a da:

  • Kifi
  • Ganyayyaki kamar su alaiyahu da salak da zogale da sauransu
  • Kayan itatuwa na marmari
  • Cin naman kaza ban da kitsen jikinta wato fata a maimakon yawan cin jan nama
  • Abinci mai dauke da sinadaran proteins kamarsu waken suya a maimakon kwai da sauransu
  • Sannan yana da kyau a riÆ™a tsinka jini don zai taimaka wajen rage cututtuka, a cewar Likitar.
Bayanan hoto,
Kayan marmari ma ana so a dinga cin su sosai idan an haura shekara 40

Wasu labarai masu alaƙa

Abinci da ya kamata mutum ya rage ci da zarar ya kai shekara 40

  • A rage cin kayan abincin cikin gwangwani
  • A rage shan lemukan kwalba, a maimakonsu a ringa shan su zobo da zai taimaka wajen gina jiki da su kunun zaki da kunun aya da lemukan kayan itatuwa, a kan wadancan na kwalbar da za su iya illa ga lafiya
  • A rage cin gishiri haka ba a cikin abinci ba, wato Æ™rin gishiri a abinci
  • A rage cin nama da kitse da goro da man shanu da cukwui.

Likitar ta kuma ce zayyana wadannan abinci ba yana nufin an ce a daina ci gaba daya lokaci daya ne ba amma za a iya fara rage ci a hankali har a daina ci musamman masu hawan jini da ciwon suga.

Duk da cewa ƙwarraru na shawartar cewa idan lafiyar mutum ƙalau ba a ce ya daina cin wani abu ba, amma dai ya kamata idan a kai waɗannan shekaru a rage cin abinci bisa shawarwarin masana.

Sannan kula da shan magungunan gargajiya da sayen magani a kanti ba tare da likita ya umarci a sha ba duk suna da illa, a cewar likitoci.

Sun kuma ba da shawara kan muhimmanci komawa ga abincin gargajiya kamar yawan cin tuwon gero da dawa da masara da cin miyar kuka da kubewa da sauransu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Zogale na daga cikin nau’in abincin gargajiyar da ake so a yawaita ci

A guji cin abincin kanti masu sinadaran da ke da hana abinci lalacewa.

Dr Sadiya ta ce, Idan aka duba mutanen da, ba sa cututtukan zamani da ake yawaita samu, saboda suna mutunta tsarin cimakarsu ba kamar yadda a wannan zamanin ake samun wadanda ke rungumar tsarin cin abincin zamani ba.

Likitar dai na cewa cimakar gargajiya ta fi ƙara lafiya, kuma ƙaurace musu na daga cikin dalilan da suka sa a wannan lokaci ake samun yawaitar cututtuka masu hadari.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...